✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da dan shugaban APC na Borno

Hukumar ‘yan sandan jihar Borno a yau Alhamis ta tabbatar da rahoton yin garkuwa da dan shugaban jam’iyyar APC  na jihar Borno Ali Bukar-Dalorin a…

Hukumar ‘yan sandan jihar Borno a yau Alhamis ta tabbatar da rahoton yin garkuwa da dan shugaban jam’iyyar APC  na jihar Borno Ali Bukar-Dalorin a makarantar yaron da ke Maiduguri ranar Laraba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar  Mista Demian Chukwu, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a Maiduguri.

Chukwu, ya ce, masu garkuwan sun yi awan gaba da yaron ne dan shekara hudu wanda har yanzu ba a san inda suka nufa da shi ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa, a yanzu haka hukumar na ci gaba da binciken lamarin don kubutar da yaron daga hannun masu garkuwan.

Chukwu ya buqaci ‘yan siyasa da su dai na amfani da wasu hanyoyin cutarwa a tsakaninsu don wata biyan bukata ta daban.