Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Kabir Bala, ya shaida wa Gwamnatin jihar Kaduna cewa daliban jami’ar takwas na daga cikin wadanda ’yan bindiga suka yi awon gaba da su da tsakar ranar Lahadi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Sai dai Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tuni jami’an tsaro suka bazama wajen laluben maharani a yankunan kananan hukumomin Igabi da Kajuru na jihar.
- Mummunan rikici ya kaure tsakanin makiyaya da manoma a Abuja
- Kungiyar kwadago ta ki amince wa da karin farashin man fetur
- An rataye mutum 21 saboda aikata ta’addanci
Gwamnatin ta sanar da hakan ne ta bakin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, wanda ya bayar da tabbaci a kan lamarin tare da yin karin haske kan wasu hare-hare da ’yan bindiga suka kai kauyen Albasu na karamar hukumar Igabi da kuma na Mararrabar Kajuru a daren ranar Lahadi.
A cewar Aruwan, hukumomin tsaro sun sanar da Gwamnatin cewa sun bazama wajen bankaso masu ta’adar tare da ba ta tabbaci a kan ci gaba da sanar da ita duk wani hali da ake ciki.
Sanarwar ta ce “a ranar Litinin ne ’yan bindiga suka kai hari kauyen Albasu da ke Yammacin dajin Malum a garin Sabon Birni kuma suka kashe wasu mazauna kauyen.”
“Haka kuma a daren ranar Lahadi, ’yan bindiga sun kai hari Mararrabar Kajuru inda suka yi garkuwa da mutum tare da harbe wani mutum daya da ya yi yunkurin tsere wa cikin dokar daji.”
“Gwamna Mallam Nasir El-Rufai ya aike da sakon jaje ga ’yan uwan wadanda abun ya shafa tare da rokon Mai Duka ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.”
Aruwan ya ce dakarun soji da ke sintiri a yankunan kananan hukumomin Chikun da Kajuru sun tsinto gawar wani dan ta’adda da ya mutu a sakamakon harbin bindiga da wasu ababe a tattare da gawarsa ciki har da bindiga kirar Ak-47.