✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi gakuwa da ’yar Sauraniyar Kudancin Kaduna

Mahara a kan motoci da babura ne suka shiga yankin suna harbi babu kakkautawa, kafin su yi awon gaba da matar

’Yan bindiga sun yi gakuwa da ’yar Saurauniyar Ikulu a Masarautar Fadar Ikulu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Mahara kusan 30 a kan motoci da babura ne suka shiga yankin suna harbi babu kakkautawa, kafin su yi awon gaba da matar, mai suna Benifica Haruna, kafin wayewar garin Talata.

Mahaifiyar gimbiyar, wadda ita ke rike da sarautar Saurauniyar Ikulu, ta bayyana cewa ’yar tata tana daki lokacin aka fara harbe-harben.

“Sai ta kira ni ta ce in samu wuri in boye, ba mu sani ba ashe mu suke nema,” in ji mahaifiyar, wadda ta ce ’yan bindigar sun kusa awa biyu suna cin karensu babu babbaka, jami’an tsaro ba su kawo dauki ba.

Don haka ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin gano inda ’yar tata take, su kubutar da ita.

Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sanda na jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige ko zai samu karin baya, amma har zuwa lokacin da aka kammala wannan labarin babu amsa.