✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi bikin neman taimakon gina gidan marayu a Kaduna

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi bikin neman taimakon gina sabon gidan marayu da kungiyar Masallacin Waff Road ta shirya a zauren…

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi bikin neman taimakon gina sabon gidan marayu da kungiyar Masallacin Waff Road ta shirya a zauren taro na Arewa House da ke Kaduna domin gina gidan marayu a Kinkinau.
Taron ya samu hallatar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu, inda a jawabin da ya gabatar ya jaddada muhimmancin taimakon marayu.
Ya ce kowa ya cancancin ya tallafi maraya saboda rauninsa. “Addinin Musulunci ya bayyana maraya ga wanda ya rasa mahaifinsa lokacin da bai balaga ba,” inji shi.
Daga nan sai ya ce akwai bukatar a yi maganin toshen matsalar da take haddasa maraici a tsakanin al’umma.
Sauran manyan bakin da suka samu halartar taron sun hada da: Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar Masallacin Waff Road Alhaji Umar Mutallab da Malam Kabir dangogo da Fasto James Wuye da sauran manyan baki da dama.
Har ila yau, an samu gudunmuwa mai yawa daga  jama’a da dama ciki har da tsofaffin shugabannin kungiyar wadanda suka ba da miliyan takwas da Fasto James da ya ba da dubu 10. Hakazalika, akwai wadansu da suka ba da gudunmuwa, amma suka bukaci a sakaya sunayensu.