’Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya 15 a Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Maharan sun kai farmakin ne a hanyar Tsakskiya zuwa Ummadau da tsakar ranar, inda suka yi wa matafiyan da ke hanyarsu ta dawowa daga kasuwa kwanton bauna, a ranar Lahadi.
- Gwamnati za ta aurar da karuwai a Bauchi
- Yadda Musulmi suka fara azumin Ramadan a bana
- Kar a manta da talakawa a lokacin Azumi — Buhari
Wani ganau ya ce “Su kusan 20 ne dauke da muggan makamai suka yi awon gaba da mutum 15 daga cikin mutum 18 da ke cikin motar. Fasinjojin suna dawowa ne daga Kasuwar Jibia, kuma yawancinsu ’yan kasuwa ne.”
Wani shaida ya ce ’yan bindigar na ganin motar, sai suka fara harbi a iska, suka razana matafiyan kafin su yi garkuwa da su.
Don haka suka bukaci hukumomin tsaro da su tsananta yin sintiri a kauyukan Karamar Hukumar Safana da sauran wadanda matsalar ’yan bindiga, masu garkuwa mutane da sauran masu aikata laifi da ke addabar Jihar Katsina.
Sai dai kuma kakakin ’yan sanda a Jihar, Gambo Isah, ya ce mutum tara ne aka sace, kuma Rundunar Operation Puff Adder ta riga ta kubutar da hudu daga cikinsu.
“Sun yi nasarar ceto hudu daga cikin fasinjojin, ragowar biyar din kuma ’yan bindigar sun yi awon gaba da su, amma ana ci gaba da kokarin kubutar da su,” inji shi.