Rumufuna 14 ne suka kone kurmus yayin da aka yi asarar kayayyakin da aka kiyasta sun kai na Naira miliyan daya da rabi a gobarar da aka yi a wani sashi na Kasuwar Kafanchan a daren Talatar da ta gabata.
Yayin da yake yi wa Aminiya bayani, Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Salisu Idris ya ce, gobarar wacce ake zargin ta tashi ne sanadiyyar wutar lantarki da ake daukewa a kawo, jama’a da jami’an tsaro sun kai dauki har aka ci karfin wutar, kafin daga baya jami’an kwana-kwana su karasa kashe ragowar wutar.
Shugaban ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa wadanda gobarar ta shafa, kasancewarsu kananan ’yan kasuwa.
Shi ma da yake jawabi bayan kai ziyarar jajantawa a safiyar Talata, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Mista Peter Danjuma Aberick ya yi alkawarin tallafa wa ’yan kasuwar, inda ya yi musu fatan Allah Ya kiyaye na gaba.