✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi artabu tsakanin jama’a da’yan Kungiyar Ba-beli a yankin Ningi

Kimanin ’ya’yan wata kungiya da ke da’awar yaki da barayi da masu garkuwa da mutane da ake kira Kungiyar Ba-Beli sama da 700 a kan…

Kimanin ’ya’yan wata kungiya da ke da’awar yaki da barayi da masu garkuwa da mutane da ake kira Kungiyar Ba-Beli sama da 700 a kan babura sama da 500 ne suka far wa mutanen kauyen Diwa a kasar Hakimin Burra da ke Masarautar Ningi a Jihar Bauchi, inda hakan ya jawo fafatawa da mutanen kauyen.

Mutum 10 ne aka ce sun ji rauni inda aka kashe daya daga cikin ’yan Kungiyar Ba-belin, sannan aka kama babura 30 da bindigogi uku da sauran makamai.

Shugaban ’Yan Bagar kauyen mai suna Shugaba Sa’adu Diwa, ya ce suna cikin gudanar da harkokin kasuwancinsu a ranar 9 ga Afrilu ne sai ’yan Kungiyar Ba-Belin suka kai hari ga al’ummar kauyen, inda su kuma suka kare kansu.

Sa’adu ya ce lamarin ya faru a ranar bayan Sallar Azahar “Sai muka ga babura da yawa kafin kiftawa da Bismilla sun kewaye kasuwarmu dauke da makamai na gargajiya da bindigogi, sai suka kama dukan jama’a. Da yake ranar kasuwa ce, babu wani abin kariya a hannun kowa, sai muka kai rahoton aukuwar hakan ga jami’an tsaro, cikon ikon Allah zuwan jami’an tsaro sai aka tarwatsa su,” inji shi.

Ya ce a lokacin harin “Sun jikkata mana mutum biyar, ciki har da wani Malam Hussaini da Dabo da Auwalu da sauransu.”

Ya ce, sun kama mutum biyar daga cikin maharan wanda daya ya mutu sauran hudu kuma suna hannun ’yan sanda.

Sa’adu, ya ce babban abin da ke faruwa a tsakaninsu da ’yan Ba-Beli shi ne, “Dajin Falgore babban daji ne da ya hada jihohi hudu, mu kuma mun tashi tsaye muka ce lallai ba za mu bar wadansu ’yan ta’adda su rika cin karensu babu babbaka a cikin dajin ba, muna taka musu birki daga yin garkuwa da mutane da fashi da makami da sauransu, kila ba su son hakan ne ya sanya suke kawo mana hari,” inji shi.

A jawabin Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya wanda ya ziyarci yankin don jajantawa kan lamarin, ya ce koda wasa ba za su amince da yawan kai hare-hare da ’yan Kungiyar Ba-Beli ke yi ga jama’ar masarautarsa ba.

Sannan ya hori mutanen masarautar su guji daukar doka a hannunsu, Sarkin ya ce ba daidai ba ne wadansu tsirari su rika kokarin kawo tashin hankali a cikin al’umma, duk mai neman fada da Ningi ya sani ba a cin Ningi da yaki, “Mun samu labarin abin da ya auku a ranar Litinin din makon jiya, mun zo domin mu jajanta muku da addu’ar Allah Ya tsayar gaba,” inji Sarkin.

Alhaji Yunusa ya tunatar da al’ummar kan muhimmancin zama lafiya inda ya ce ba wani ci gaban rayuwa da za a samu sai da zaman lafiya. “Dole ne jama’a su kasance masu bin doka da oda a kowane lokaci, Mun samu labarin cewa mutanen da suka kawo muku hari sun kai 700, a kan babura sama da 500. Kun yi kokari wajen kare kanku da maida martanin da ya dace. Duk da ba mu so haka ba, bai dace su fado cikin garinku su auka muku ba, ku kuma bai dace ku yi fada da su ba.”

Sarkin Ningi ya ce a mika babura 30 da sauran kayan fadar da mutanen suka kama ga ’yan sanda, “Wadanda suka kawo muku harin nan ba ’yan fashi ba ne, wata kungiya ce da suka hada kansu wai su ’yan Ba-beli; to mu a Masarautar Ningi ba mu yarda da wannan kungiyr ta Ba-Beli ba,” inji shi.

Sarkin ya jawo hankalin kungiyoyin sa-kai cewa su rika tafiyar da ayyukansu bisa dokar da aka tsara kuma su rika kai rahoton aukuwar wata matsala ga jami’an tsaro cikin lokaci domin daukar matakan da suka dace.

Kwamanda ’yan sandan shiyyar Bauchi ta Tsakiya, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Mukhtar A. Idris ya ce a kowane lokaci suna fata kowane mutum ya kasance mai bin doka da oda, kuma a shirye suke su rika gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro da kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Ya ce, “Duk wanda ya taka doka, doka za ta yi aiki a kansa komai mukamin mutum, amma dai abin da ake so duk abin da mutum zai yi ya tabbatar ya yi ne a karkashin doka.”

Ya ce ’yan sanda za su tabbatar da kare lafiyar jama’a kuma za su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin hakan bai kara faruwa ba.