✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi addu’o’i na musamman ga Najeriya a dutsen Arafa

Sananne ne cewa akwai tabbaci kan karbar addu’ar da aka yi a dutsen Arafa da kewayenta. Kuma yadda addu’a take magance wasu abubuwa da ba…

Sananne ne cewa akwai tabbaci kan karbar addu’ar da aka yi a dutsen Arafa da kewayenta. Kuma yadda addu’a take magance wasu abubuwa da ba a so ko suke jawo matsaloli aba ce da ba za a yi wasa da ita ba. Kasancewa a harabar Arafa  a ranar 9 ga watan 12 ta shekarar Musulunci, shi ne kirjin aikin Hajji ga wadanda suke can da kyakkyawar niyya na sauke farali. Kuma aikin da ake bukata daga mahajjaci shi ne ya himmantu ga tsarkake kansa da kuma sadaukar da rayuwarsa ga bautar Allah: kamar Sallah da addu’o’i da istigfari da neman rahama da jin kan Allah tare da sauya tunani da rayuwar mutum don ya zamo nagari a bayan haka. Wannan yana gudana ne a tsakanin fitowar rana da faduwarta a waccan rana.

Babban lamari! Al’adar Hukumar Hajji ta kasa ce (NAHCON) ta yi amfani da wasu awanni na wannan muhimmin lokaci wajen yin addu’o’in rokon Allah Ya kyautata harkokin mulki tare da yi wa shugabannin Najeriya jagoranci. Addu’ar da aka gudanar ga kasar nan a bana a filin Arafa ta fita daban, inda mahajjatan jihohi a cikin tantunansu suka yi irin wadannan addu’o’i ga jihohinsu da kuma kasa baki daya kamar yadda hukumar ta bukata.

Baya ga haka an gudanar da addu’a ta kasa a cikin harsuna daban-daban inda aka roki Allah Ya gaggauta ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari da rokon Allah Ya yi masa jagora tare da kare shi da kuma kara masa ilimi da hikima da karfin halin gudanar da ayyuka nagari don sake fasalin Najeriya ta yadda zai kai ta tudun mun tsira.

Maso ibada sun roki Allah Ya ba Shugaba Buhari mashawarta nagari masu sakakkiyar zuciya da za su taimaka masa wajen sauke nauyin farfado da tattalin arzikin kasar nan da harkokin rayuwar ’yan Najeriya tare da samun shugabanni nagari da mabiya nagari tun daga sama har zuwa matakan jihohi.

An gudanar da addu’o’in ne a tantin Jihar Edo inda aka yi addu’o’i ga dukan gwamnonin jihohi 36 da Ministan Birnin Tarayya da majalisar dokoki ta kasa da bangaren shari’a da majalisun jihohi. 

Kafin fara addu’o’in wadanda aka dauki awa daya ana yi, Shugaban Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Birista Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya bukaci babban jami’i mai da harkokin ofishin Jakadancin Najeriya da ke Riyadh Salisu Umar da karamin jakadan Najeriya a Jeddah Amsabada Muhammad Sani Yunusa, sun yi bayanai don tunatar da mahajjatan kan dalilan da suka kawo su filin Arafa da kuma irin garabarsa da Allah Ya shirya musu a matsayinsu na ’yan Najeriya.

Barista Muhammad ya bukaci malaman da aka zaba daga cikin ayarin malaman kasa da su yi wa Shugaba Buhari addu’a da kuma yi wa kasa addu’ar kasancewa a dunkule da farfadowar tattalin arziki Najeriya. “Wannan wuri ne mai tsarki da ake amsar addu’o’i. Ina fatan za mu yin amfani da wannan babbar dama wajen rokon Allah Ya ba Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari lafiya kuma ya bunkasa mana tattalin arzikinmu. Dukanmu muna son hadin kai da zaman lafiya da cin gaban Najeriya,” inji shi.

Jakadun biyu sun bunkaci ’yan Najeriya su guji furta kalaman nuna kiyayya ga juna da duk wani hali da zai kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kan Najeriya. “Ba mu da wata kasa fiye da Najeriya wadda muke alfahari da ita. Don haka mu yi mata addu’a da shugabanninta da dukan mutanenta, kan Allah Ya yi musu jagora kuma Ya kare su,” inji su.

An fara gudanar da addu’o’in ne da harshen Larabci wadda Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya gabatar, sai Dokta Mansur Ibrahim ya gabatar da Ingilishi, sai Sheikh Musa Najmudeen ya gabatar da Hausa, Farfesa Khalil Kayoyo ya gabatar da Yarbanci, Dokta Aminu Igwegbe ya gabatar da Ibo. Sauran harsunan da aka gudanar da addu’o’in da su, sun hada da Fulatanci da Bini da Tibi da Barbarci, inda fitattun ’yan Najeriya da dama suka halarta.