✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi addu’ar kawo ƙarshen zanga-zanga a Yobe

Goni Modu Aisami ya ce yawancin yaran da suka shiga zanga-zangar ba almajiransu ba ne.

Hukumar Kula da Harkokin Addinin Musulunci da Harshen Larabci ta Jihar Yobe ta shirya taron addu’a na yini guda domin neman Allah Ya kawo ƙarshen zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a faɗin kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda suka shirya taron sun gudanar addu’ar Allah Ya kawo ɗauki dangane da halin matsin rayuwa da ake fuskanta a yanzu.

Hukumar ta kuma nemi malaman tsangaya da su tsawatar da ɗalibansu kan illar shiga zanga-zangar da ake gudanarwa.

Da yake zantawa da Aminiya a wajen taron addu’o’in a Damaturu, Sakataren Zartarwa na hukumar, Umar Abubakar, ya ce sun gayyaci shugabannin makarantun Tsangaya na jihar ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Goni Modu Aisami domin yi wa Jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya da kawo ƙarshen tsadar rayuwa da al’umma ke fama.

Ya buƙaci ɗaukacin iyaye da malamai a jihar musamman waɗanda ke da almajirai da su tausasa su kan su yi watsi da zanga-zangar da ake yi a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, halin da ake ciki a ƙasar na buƙatar addu’a, inda malaman suke ci gaba saukar karatun kur’ani mai tsarki yayin da wasu kuma suke addu’o’in neman zaman lafiya a ƙasar.

“Muna jan hankalin ƙungiyar makarantun tsangaya da ke jihar domin mu sanar da su haƙiƙanin abin da ya faru cewa an samu wasu almajiranmu da suka shiga zanga-zangar da ake yi.

“Gwamnatin Yobe ta riga ta samar da kayayyakin abinci na kwana biyar ga ɗaukacin ɗaliban makarantun tsangaya a faɗin jihar domin a ci gaba da zama a gida don kada su shiga zanga-zangar da ke gudana,” inji shi.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar makarantun tsangaya reshen Jihar Yobe, Goni Modu Aisami, ya ce yawancin yaran da suka shiga zanga-zangar ba ɗalibansu ba ne.

“Yawancinsu ’ya’yan talakawa ne a cikin al’umma.

“Ni da kaina na ga yara suna riƙe da kwano suna zanga-zanga a Damaturu, amma da na tambaye su ko Almajirai ne, sai suka ce a’a,” inji Goni Modu.

Goni Aisami ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta zakulo wadanda suka fi kowa rauni a cikin al’umma tare da taimaka musu wajen ɗaukar nauyin ’ya’yansu yadda ya kamata.