Sabbin kwararan soji 4,828 da suka samu horo daga Makarantar Horas da Kuratan Sojin Kasa da ke Zariya ne aka yaye a Asabar.
Da yake jawabi wurin bukin yaye sabbin sojojin, Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruq Yahaya ya hore su da su kasance masu amfani da horon da suka samu wurin kokarin kawar da ayyukan ta’adanci a kasar nan.
- ‘An kulle’ sojar da bidiyon neman aurenta da dan NYSC ya karade gari
- Jami’an kwastam sun kama kwantaina makare da bindigogi daga kasar waje
Ya ce Najeriya na fuskantar kalubale da dama da suka hada da na kungiyar Boko Haram da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Janar Faruq Yahaya ya kara da cewa rundunar soji na iya bakin kokarinta wurin kawar da su a sassan kasar.
Ya hori sabbin sojin da sauran dakarun rundunar da su ci gaba da kasancewa jakadu na gari domin kare martabar Najeriya a ko’ina suke.
Ya mika godiyarsa ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari bisa kokarin da yake yi domin wadata rundunar da kayan aiki saboda fuskantar ayyukan da ke gabanta.
Jim kadan bayan kammala bukin yayen, Babban Hafsan ya kaddamar da wani dakin taro da wurin shakatawa da aka sanyawa sunan Misis Saratu Chinedu.