Wata babbar Kotu a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, ta yanke wa wani mutum mai shekaru 33, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Yayin da yanke hukuncin a ranar Juma’a, Alkalin kotun Mai shari’a Abiodun Akinyemi, ya ce laifin da mutumin ya aikata ya wuce duk wani tunanin mai tunani.
- Ba a sako Daliban Kagara ba —Gwamnan Neja
- An rufe bankuna uku a Maiduguri
- Dalilin ’yan mata na son auren mai mata fiye da saurayi
Akinyemi ya ce kotun bayan samun mutumin da aikata fasadi doron kasa na kashe wani abokinsa aikinsa, wannan laifin ya saba da sashe na 317 na kundin dokokin miyagun laifuka na Jihar Ogun da aka kirkira a shekarar 2006.
“Saboda haka kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar,” in ji Mai shari’a Akinyemi.
Tun da fari, ’yar sanda mai gabatar da karar a gaban kotu, Misis Oluwaseni Ogunjimi, ta bayyana cewa, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Satumbar 2013, da misalin karfe 9 na dare a shatale-talen Atala da ke Bolatito a yankin Mowe da ke Jihar Ogun.
Misis Ogunjimi ta ce wanda ake tuhumar ya harbe wani abokinsa na wata masana’anta a kan hanyarsa ta dawowa daga sayen ruwan leda.
Ta ce an garzaya da mutumin da aka harba mai suna Tosin Joye zuwa Asibiti don kawo samun kulawa ta gaggawa amma daga bisani ya ce ga garinku nan.