✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa ’yan ta’adda 200 hukuncin kisa da ɗaurin rai-da-rai

An yanke wa ’yan ta'adda da masu ɗaukar nauyinsu sama da 200 hukuncin kisa da ɗaurin rai-da-rai a cibiyar da ake tsare da su a…

An yanke wa sama da mutum 200 hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai kan ayyukan ta’addancin da masu ɗaukar nauyinsu a faɗin Nijeriya.

Alƙalan Manyan Kotunan Tarayya ne suka yanke musu hukunci bayan an gurfanar da waɗanda ake zargi, inda ka samu mutane 500 da laifin da ke da alaka da ayyukan ta’addanci.

Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro ne ta gurfanar da su a cibiyar da ake tsare da su a yankin Kainji da ke Jihar Neja.

Ofishin ya bayyana cewa daga cikin mutanen akwai waɗanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 20 zuwa shekaru 70, gwargwadon girman laifin da aka same su da shi.

Da yake bayani kan kammala shari’ar rukuni na 6 na waɗanda ake zargin, Ofishin ya bayyana cewa daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Disamban nan da muke ciki, an gurfanar mutum 237 da ake tsare da su a cibiyar.

Ofishin ya sanar a ranar Lahadi cewa waɗanda aka yanke wa hukunci mafi tsanani su ne waɗanda aka kama da laifin yi wa mutane yankan rago da garkuwa da mutane a yankin Gina Kara Kai da ke Jihar Borno.

Suran su ne waɗanda aka samu da laifin kai wa mata da ƙananan yara hari da kuma lalata wuraren ibada.

“Bayan su, an yanke wa wasu masu ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci hukuncin kisa.

“Wannan babbar nasara ce a yayin da gwamnati ta duƙufa wajen murƙushe ayyukan ta’addancin Boko Haram da kungiyar IPOB da ’yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci da tayar da ƙayar baya a kasar nan,” in ji sanarwar Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro.

Ta kuma jinjina wa jami’an tsaro kan namijin ƙoƙarinsu wajen taka burki ga duk wata barazanar tsaro da ta kunno kai.

Haka ma fannin shari’a da ke gurfanar da waɗanda ake zargi domin a yanke hukunci bisa adalci, kowa ga girbi abin da ya shuka.