Kotu ta yanke wa wani matashi mai shekara 26 hukuncin daurin rai-da-rai bayan samun shi da laifin yi wa ’yar makwabcinsa fyade.
A ranar Alhamis kotun da ke jihar Legas ta yanke wa matashin bayan ta bayyana cewa ta gamsu cewa wanda ake zargin ya sha yi wa yarinyar fyade a cikin bandaki.
- Yadda likita ya yi wa mara lafiya fyade a asibiti
- Yadda aka kama miyagun kwayoyi miliyan 8.2 a Saudiyya
Alkali Abiola Soladoye ta ce bayanan duk da kokarin matashin na wanke kansa, yarinyar da kuma rahoton binciken da ’yan sanda suka gabatar sun gamsar da kotun cewa ya aikata laifin.
Ta ce, “yarinar ta gabatar da gamsassun bayanai kan yadda ya rika yi mata fyade a cikin bandaki, sannan ya kuma bukaci kada ta bari kowa ya sani.
“Baya ga haka, ta bayyana yadda ya sha yi mata fyade a lokutan da take zuwa dakinsa domin yin kallo a wayarsa kasancewarsa makwabcinsu.’
Don haka ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai ta kuma ba da umarnin a sanya sunansa a kundin jerin mutane masu lalata kananan yara na jihar Legas.
Ta kuma bukaci hukumoi da abin ya shafa da su ci rika wayar da kan iyaye a wurare daban-daban game da muhimmancin lura da ’ya’ansu domin kare su daga masu yi wa kananan yara fyade.