✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa Oscar Pistorous daurin shekara 6 kan kashe budurwarsa

dan wasan tseren nakasassu dan Afirka ta Kudu, Oscar Pistorous da ya kashe budurwarsa ta harbinta da bindiga a shekarar 2013 zai je shafe shekara…

dan wasan tseren nakasassu dan Afirka ta Kudu, Oscar Pistorous da ya kashe budurwarsa ta harbinta da bindiga a shekarar 2013 zai je shafe shekara shida a gidan kaso.
Pistorous wanda ya kashe budurwarsa Reeba Steekamp mai shekara 29 a Ranar Masoya na shekarar 2013 ta harbin ta da bindiga, kotu ta same shi ne da laifin kisan gilla.
dan wasan tseren wanda bai da kafafu, ya samu nasara sosai inda ya yi fice a harkar wasan tseren nakasassu ta hanyar amfani da kafar roba.
Pistorous ya ce ya yi kuskure wurin harbe budurwarsa domin ya dauka wani ne daban ba ita ba, sannan ya ce yaya zan kashe budurwata da nake so?
Mai shari’a Thokozile Masipa na Babbar Kotun Gauteng ta Yamma ne ya yanke hukuncin bayan an dauki sama da shekara uku ana fafatawa.
Alkalin ya ce, juyayi da nadama ne suka sa aka rage yawan shekarun da ya kamata a yanke wa wanda ya yi kisan daga shekara 15 zuwa shekara 6. Sannan wanda aka yanke wa hukuncin yana da damar daukaka kara.