Mutum 30 a ranar Asabar aka yanke wa hukuncin kisa sakamakon wani rikici da ya barke kan jagorancin sallar Idi a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.
Rikicin wanda ya barke ranar Alhamis a Kinshasha, babban birnin kasar tsakanin bangarorin Musulmi biyu masu sabani da juna, ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan sanda daya da jikkatar gommai.
- JAMB ta sauya ranar jarrabawar bana, ta tsawaita wa’adin rajistar dalibai
- El-Rufai da Kungiyar Kwadago sun sa zare a Kaduna
Kafofin watsa labarai da dama sun ruwaito cewa, rikicin ya tashi ne sakamakon sabani tsakanin bangarorin musulmin dangane da wanda zai jagoranci sallar Idi bayan kammala Azumin Ramadana.
Shugaban rundunar ’yan sandan kasar, Sylvano Kasongo, wanda ya takaice bayar da misalin rikicin a matsayin mai munin gaske, ya ce jami’an ’yan sanda 46 aka jikkatar da kuma gomman motocinsu da aka kone.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, an yi mummunan tashin hankalin ne a wajen filin wasa na Martyr’s inda a nan ne za a gudanar da sallar Idin wanda jagoracinta ya janyo sabani.
Mutum 49 aka gurfanar gaban Kuliya wanda aka rika nuna zaman shari’ar kai tsaye a gidajen talabijin duk tsawon dare.
Rahotanni sun ce daman akwai dadadden sabani kan neman shugabancin al’ummar Musulmi a wannan yanki na kasar tsakanin kungiyoyi biyu da ke sabani da juna.