Wata babbar kotu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani matashi mai suna Kamal Yusuf bayan samun shi da laifin kashe mahaifiyarshi da kuma kannen shi mata guda biyu.
Gwamnatin jihar Zamfara ce dai ta gurfanar da matashin a gaban kotun jihar tare da wasu mutum biyu wato Armayau Shehu da kuma Caleb Humphrey tana tuhumar su da aikata laifuffuka guda uku.
To sai dai daya daga cikin wadanda ake tuhuma din Caleb Humphrey ya mutu yayin da ake sauraren shariar.
Laifuffukan dai sun hada da hada baki domin aikata laifi, da fashi da makami da kuma aikata kisan kai, wanda kuma hukuncinsa kisa ne matukar an samu wanda ake zargi ko tuhuma da aikata laifin.
- An kama ’yan matan da ke yi wa ’yan bindiga leken asiri a Zamfara
- Matashi ya kashe mahaifinsa a kan kosan bude-baki
Da take yanke hukuncin, babbar jojin jihar ta Zamfara Mai Sharia Kulu Aliyu ta samu Kamal Yusuf da aikata laifukan ta kuma yanke mashi hukunchin kisa ta haryar rataya, a yayin da kuma ta wanke Armayau Shehu daga dukkan zargi ta kuma sallame shi.
Idan dai za a iya tunawa a shekarar 2013 aka kama Kamal Yusuf da abokanshi biyu bisa zargin kisan mahaifiyarshi Hajiya Hafsatu da kuma kannenshi mata Maryam da Amina.
Kamal ya yi fushi da mahaifiyar tashi ne bayan da ta ki yarda ta ba shi dukiyar da kannensa suka gada daga mahaifinsu, wanda ta aura bayan rabuwar ta da mahaifin Kamal.
An zargi Kamal da gayyato abokansa suka kuma kashe mahaifiyar tashi da kannen sa, suka jefa gawarwakin a cikin babbar madatsar ruwa ta Gusau.
Yana da damar daukaka kara nan da kwana casa’in.