Wata Babbar Kotun Akwa Ibom da ke zamanta a yankin Ikot Ibritam na Karamar Hukumar Orum Anam, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Aminiya ta ruwaito cewa, kotun ta yanke wa Akaninyene Sunday Ekwere mai shekaru 32 hukuncin ne bayan samunsa da laifin fyaɗe.
Bayanai sun ce matashin mai sayar da baƙin mai, kayayyakin lantarki da katin waya ya zakke wa wata karamar yarinya ce a shagon sana’arsa.
Mista Ekwere dai kamar yadda kotun ta tabbatar, ya yaudari yarinyar mai shekaru huɗu kacal, inda ya shigar da ita shagonsa ya yi lalata da ita.
Tunda farko mahaifiyar yarinyar ce ta gano rauni a jikin diyarta yayin da take mata wanka, lamarin da iyayenta suka yi gaggawar kai wa ’yan sanda korafi.
A ƙunshin bayanan da ya gabatar a kotu, Ekwere ya ba da rahoton yadda ya soma hango yarinyar tana wasa a kusa da shagonsa.
Hakan kamar yadda ya shaida wa kotun ce ta sanya Ekwere ya yi kiranta, inda ya shigar da ita shagonsa kuma ya shafa mata man shafawa a gabanta sannan ya yi mata fyaɗe.
Da yake yanke hukunci, alkali Nkereuwem Obot, ya ce Ekwere bai cancanci zama a cikin mutane masu hankali ba saboda hatsarin da yake tattare da shi.
A bisa wannan hujjar ce Kotun ta yanke wa Ekwere hukuncin zaman Gidan Dan Kande na tsawon rayuwarsa.
Mista Ekwere wanda ya shahara da sunan “Doctor” ya nemi Kotun ta yi masa sassauci kasancewarsa magidanci mai iyali, roƙon da kotun ta yi biris da shi.