✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa Lionel Messi ‘daurin wata 21’ a Spain

An yanke wa dan wasan kwallon kafa na kasar Ajentina da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain, Lionel Messi…

An yanke wa dan wasan kwallon kafa na kasar Ajentina da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain, Lionel Messi daurin wata 21 a gidan kurkuku a kasar Spain kan samunsa da laifin yin almundahana wajen biyan haraji.
Gidan rediyon BBC ne ya ruwaito kafofin watsa labarai na kasar Spain suna bayyana haka a shekaranjiya Laraba.
BBC ya ce an kuma yanke wa mahaifin Messi mai suna Jorge Messi, hukuncin dauri na wani lokaci da bai ambata ba, kan damfarar kasar Spain Fam miliyan hudu da dubu 100 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 845) a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.
A yayin shari’ar masu gabatar da kara sun ce an rika amfani da kasashen Belize da Uruguay da ba su karbar haraji kan dukiyar da ake ajiyewa a can wajen boye hakikanin dukiyar da Messi ya mallaka a Spain.
Sai dai Messi ya ce, “bai san komai” game da harkokin kudinsa ba.