Wata kotun sauraron ayyukan cin zarafi da ke zamanta a Ikejan Jihar Legas, ta yanke wa wani likita, Olufemi Olaleye, hukuncin daurin rai da rai saboda samunsa da laifin yi wa ’yar uwar matarsa fyade.
Likitan dai shi ne shugaban Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Optimal da ke Jihar ta Legas.
- Jami’an tsaro sun kama AK-47 guda 150 a gidan dan ta’adda a Neja
- Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 5,000
Alkalin kotun, Mai Shari’a Rahman Oshodi ne ya samu likitan da lalata yarinyar ta hanyar yi wa yarinyar mai shekara 15 fyade.
Ya ce masu shigar da kara sun gamsar da kotun da hujjojin da suka gamsar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin. An dai gurfanar da shi ne a gaban kotun ranar 30 ga watan Nuwamban 2022, kodayake ya musanta aikata laifin.
Daraktan Ofishin Gurfanar da masu laifi na Jihar, Babajide Martins, ya shaida wa kotun cewa Olaleye ya aikata laifin ne a tsakanin watan Fabrairun 2020 zuwa Nuwamban 2021, a layin Layi Ogunbambi da ke unguwar Maryland.
An kuma zarge shi da saka wa yarinyar gabanshi a cikin bakin yarinyar.
Laifin, a cewar masu shigar da karar, ya saba da tanade-tanade sassa na 137 da da 261 na Kundin Manyan Laifuffuka na Jihar Legas na shekara ta 2015.