Wata Babbar Kotu ta yanke wa matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya, saboda kama sa da laifin fashi da makami.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Lekan Ogunmoye na Babbar Kotun da ke zamanta a garin Ado-Ekiti, Jihar Ekiti, ya ce kwararan hujjoji sun tabbatar da laifin da ake zargin matashin.
- Saudiyya ta kashe matashi kan laifin da ya aikata yana karami
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 26 a kauyen Zamfara
Sai dai kuma tun a watan da ya gabata alkalin ya sallami sauran mutum uku da ake zargi da aikata fashin tare da matashin.
Mai gabatar da karar ya ce matashin tare da wasu sun aikata fashi ga Dayo Folorunsho, Saka Yusuf, Adeoye Oluwatosin, Adeola Oluwatobi, Olayemi Aremu, Hambali Ojo da Ayodele Oluwafemi, a watan da ya gabata.
Bincike ya nuna sun saci wayoyin hannu, mota kirar Lexus E5 350, katin cirar kudi (ATM), babur kirar Bajaj, agogon hannu da kuma tsabar kudi N205,500.
Lauya mai shigar da kara, H.A Adeyemi, ta gabatar da shaidu kan wanda ake tuhumar, wanda kuma aka samu karamar bindiga kirar gida, akwatunan harsasai biyu, da sauran makamai. (NAN).