Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya roki jami’an tsaro a jihar su dawo da dokar hana fita don maganin ayyukan ’yan ta’adda.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Kwamandan Rundunar Soji ta 2 a jihar, Manjo Janar Anthony Bamidele Omozoje.
- An sace Shugaban Karamar Hukuma da wasu mutum 13 a Edo
- ’Yan kungiyar asiri sun hana Jihar Edo sakat
- ‘Yan bindiga sun sace mutum 8 a Edo
- Gidan tarihin Birtaniya ya ba da $4m don gina gidan tarihi a Edo
“Yanzu dole mu sake dawo da dokar kulle daga 10 na dare zuwa 6 na safe; Duk wanda aka samu a waje lokacin dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani.
“Za mu yi amfani da kwanaki bakwan wajen kama wadannan bata-garin sannan a dawo da makaman da suka sace daga hannun jami’an tsaro”, cewar Obaseki.
Gwamnan ya ba wa rundunar sojin tabbacin hadin kai da kuma tallafi don ganin an dakile ayyukan ta’addanci da suka addabi jihar tun bayan kammala zanga-zangar #EndSARS.
Obaseki ya ce hakan aka yi a jihohin Kwara, Oyo, Ekiti da Osun kuma duk an samu kyakykyawan sakamako.
A cewarsa bayan kammala farautar ’yan ta’ddar da suka damu jihar, za su duba nasarar lamarin kafin daukar mataki na gaba.