✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ware biliyan 4 don zuba mai a motocin ’yan sanda

An ware kudaden ne don inganta ayyukan 'yan sandan.

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan hudu don zuba mai a motocin aiki na ’yan sanda a jihohi 36 na kasar nan da Birnin Tarayya, Abuja.

SAURARI: Halin da ’yan gudun hijira ke ciki:

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan lokacin da ya gabatar da takarda game da harkokin ’yan sanda, a Cibiyar Nazarin Aikin ’Yan Sanda ta Kasa da ke Abuja, a ranar Talata.

Dingyadi ya jaddada cewa amincewa da irin wannan makudan kudade a kasafin kudin 2021 shi ne karo na farko a tarihin aikin dan sanda a Najeriya.

“Ma’aikatar tana matukar godiya ga Shugaban kasa da Majalisar Tarayya da suka amince da kudaden sayen man motocin ’yan sanda a jihohi 36 na kasar nan da Birnin Tarayya don kara inganta aikinsu; An ware sama da Naira biliyan hudu don wannan manufa,” inji shi.

Ministan ya kara da cewa Asusun Tallafin Aikin ’Yan Sanda ya ba da kwangilolin sayo karin motocin aiki, kayan kariyar jiki, makamai, harsasai, magunguna da kayan aikin likita, da sauran mahimman kayan aikin tsaro.

Ya kara da cewa ko a kwanan baya, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da ayyukan musamman na ’yan sanda don inganta gaskiya da rikon amana a tsakanin jami’ainsu.

Da aka tambaye shi game lokacin za a fara biyan sabon albashin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi musu alkawari, Dingyadi ya ce nan ba da jimawa ba Hukumar Tsara Albashi ta Kasa, za ta fitar da sabon tsarin albashin ’yan sanda mai inganci.