Gwamnatin Jihar Gombe ta shirya fara biyan hakkin ma’aikatan da suka yi ritaya a Kananan Hukumomi 11 na jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomin jihar, Abdulkadir Waziri ne, ya sanar wa manema labarai jim kadan da kammala zaman Majalisar Zartarwar jihar karo na 36.
- ’Yan bindiga sun harbe dan sanda har lahira a Zamfara
- Gwamnatin Gombe za ta biya tashar Dikku da Bauchi diyyar miliyan 332
Ya ce gwamnati ta ware sama da Naira biliyan uku don fara biyan bashin giratutin baya zuwa shekarar 2022.
Har wa yau, ya ce wasu kananan hukumomin za su biya na shekara biyu wasu zuwa sama.
Waziri, ya kuma ce baya ga wannan majalisar ta amince wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, da ya gina gidajen sarakuna a wasu kananan hukumomi da samar musu da hanyoyi.
Kazalika, gwamnatin jihar za ta kashe kashi, na adadin kudaden da za a kashe wajen ayyukan yayin da kuma uma kananan hukumomin za su kashe sauran kudin.