Majalisar dokoki ta jihar Nasarawa ta umarci sakataren gwamnatin jihar ya mayar da sama da Naira miliyan 248 asusun gwamnati.
Wani kwamitin wucin-gadi da majalisar ta kafa don ya binciki badakalar wasu kwangilolin katange makarantu ne ya umarci Aliyu Ahmad Tijjani, wanda tsohon kwamishinan ilimi ne a jihar, da ya mayar da kudin.
Kwamitin, wanda ke bincike tare da bin diddigin kimanin Naira biliyan daya da aka fitar don katange makarantun sakandire a jihar ya ce an yi wa-ka-ci-ka-tashi da kudaden.
Shugaban kwamitin, Hon. Daniel Oga Ogazi, shi ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin nasa a zauren majalisar ranar Litinin.
Ranar Talata muhawara
Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya ayyana Talata a matsayin ranar tafka muhawara a kan rahoton.
Hon. Ogazi ya ce tsohon kwamishinan ya nuna rashin kwarewa da rashin dattaku yayin gudanar da aikinsa.
A cewarsa, bincikensu ya gano cewa Naira miliyan 873 ne aka kashe a kan ayyukan da aka kammala da ma wadanda ba a kammala ba, kamar yadda kwafin rasidan biyan kudaden suka nuna.
Sai dai ya ce adadin bai kunshi kashi 5 cikin 100 na kudaden duba ayyukan ba.
“Adadin kudaden da aka bayar da kwangilar shi ne N1,084,000,000, idan ka cire N873,233,942.60, za ka ga akwai ragowar N210,766,057.40.
“Idan kuma ka tara da kashi 5 cikin 100 na kudaden duba ayyukan da suka kai N37,718,499.19, za ka ga cewa akwai kimanin N248,484,556.60 wadanda suka yi batan dabo.
Dokar ta-baci
Ogazi ya ce tuni gwamnatin jihar ta ayyana dokar ta-baci a kan dukkan kwangilolin don ganin an gaggauta kammala su.
Ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan kwangilar da suka san sun karbi kudaden da su gaggauta kammala ayyukansu cikin wata daya ko su hadu da fushin gwamnati.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 17 ga watan Maris ne majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin don ya yi bincike a kan yadda aka kashe kimanin Naira biliyan daya a kan kwangilolin katange makarantun sakandire a jihar.