✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An umarci Ma’aikatan Legas su ci gaba da aiki daga gida saboda Coronavirus

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, ya ba daukacin ma’aikatan Jihar wadanda suke mataki na 14 zuwa kasa umarnin ci gaba da gudanar da ayyukansu…

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, ya ba daukacin ma’aikatan Jihar wadanda suke mataki na 14 zuwa kasa umarnin ci gaba da gudanar da ayyukansu daga gida daga ranar 4 zuwa 18 ga watan Janairun 2021.

Hakan na kunshe ne cikin wata sabuwar sanarwa da aka fitar daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Mista Hakeem Muri-Okunola zuwa ga mambobin Majalisar Zartarwa da Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Jihar a ranar Lahadi.

Sanarwar da Gwamnatin Jihar ta fitar na zuwa ne a sakamakon yadda ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar Coronavirus wadda Mahukuntan Lafiya na Duniya suka ayyana cewa tana kan zagaye na biyu.

Takardar sanarwar mai dauke da sabon tsarin mai taken ‘Kokarin dakile yaduwar annobar COVID-19 a zagaye na biyu’ ta bayyana cewa umarnin aiki daga gida ya kebe masu gudanar da ayyuka na musamman a yayin da ake neman dukkan ma’aikatan gwamnati a Jihar da su ci gaba da kiyaye matakan kariya domin dakile yaduwar cutar a Jihar.

Alkaluman Hukumar NCDC mai Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa sun nuna cewa Jihar Legas ce a kan gaba da mafi yawan wadanda cutar Coronavirus ta harba a duk fadin Najeriya.