An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun.
Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas.
- NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya
- Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro
Ya je otal ɗin Super G Royal da ke rukunin gidaje naAnthony Uzum tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar.
Da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba.
Lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da suka zo tare ba ta cikin ɗakin.
Rahoton ’yan sanda ya bayyana cewa mamallakin otal ɗin, Abiodun Olagunju ne, ya kai rahoto ga hukumomi.
Ya kuma bayyana cewa matar da ta tsere ta je wajen masauƙin baƙi da misalin ƙarfe 6 na safe, inda ta nemi ruwan sha.
An ɗauke gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawa na Life Channel Mortuary da ke Olambe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce da farko ba gano ɗan sanda ba saboda ba a samu katin shaidarsa ba, sai bayan da aka bincika aka gano yana aiki da Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ishashi da ke Legas.
’Yan sanda sun fara neman matar da ta tsere, kuma ana ci gaba da bincike don gano dalilin mutuwarsa.