✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar yaro mai shekara 11 a rataye a Abuja

An ce ya yi hatsaniya da yayarsa gabanin faruwar lamarin

An tsinci gawar wani yaro mai kimanin shekara 11 yana reto a jikin igiyar shanya da ke tsakar gidansu a yankin Kubwa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wasu makwabta da suka garzaya da shi asibiti sun bayyana wa Aminiya cewa, yaron sun yi ‘yar hatsaniya da babbar yayarsa kan dukan kanwarsu da ya yi gabanin faruwar lamarin.

Wannan ne ya sa suke zargin shi ne abin da bai yi masa dadi ba har ta kai shi ga aikata wannan danyen aiki.

Mahaifin yaron mai suna Umar Yahaya, ya ce lokacin da lamarin ya faru, shi da mahaifiyar yaron ba sa gida.

“Ba na gari lamarin ya faru, ita ma kuma mahaifiyarsa ta tafi gaisuwar mutuwa, sai dawowa ta yi ta tarar da gawarsa.”

Yaron dai kafin rasuwarsa dalibi ne aji biyu na karamar makarantar Sakandare.

A hannu guda kuma, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Abuja ta ce ba su da rahoton faruwar lamarin.