Mazauna unguwar Badagry da ke Jihar Legas na cikin alhini bayan an gano gawar wasu kananan yara har guda takwas a cikin wata lalataccitar mota ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa yaran sun gamu da ajalinsu ne bayan sun kulle kansu a cikin motar bisa rashin sani, lokacin da suke tsaka da wasa a ciki.
- Zanga-zangar kin jinin rigakafin COVID-19 ta kara zafi a Belgium
- Tsohon Minista, Bunu Sheriff, ya rasu
Sun dai gamu da ajalinsu ne bayan duk iya kokarinsu na fitowa daga motar ya ci tura, har numfashinsu ya dauke.
Aminiya ta gano cewa wani mai wucewa ne ya ankarar da mazauna wajen halin da yaran ke ciki.
Majiyoyi sun ce bayan balle kofar motar ta karfin tsiya, an ciro gawarwakin yaran, wadanda shekarunsu ba su wuce tsakanin shida zuwa takwas ba.
Hakan dai ya jefa mutanen cikin kaduwa, tare da bukatar ’yan sanda su binciki musabbabin mutuwar.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Legas, Adekunle Ajisebutu, ya ce, “Yaran su takwas sun mutu ne bayan sun kulle kansu a cikin motar da suke wasa bisa kuskure.
“Mun kwaso gawarwakinsu zuwa babban asibitin Badagry don gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsu, kuma tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Hakeem Odumosu ya bayar da umarnin zurfafa bincike a kai,” inji kakakin.