✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar shugaban tasha a bakin rafi

Shugaban tashar kananan motoci a jihar Akwa Ibom an tsinci gawarsa a bakin wani rafi.

An tsinci gawar shugaban tashar kananan motoci na Karamar Hukumar Abak, Jihar Akwa Ibom, Samuel Bassey, a bakin rafi a wani kauye.

Ana zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kashe mamacin wanda ya je yin wanka a rafin bayan tashi daga buga wasan kwallo shi da abokinsa.

Tun da suka tafi wankan ba a sake ganin sa ba sai gawarsa da aka tsinta a bakin rafin.

Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewa, an kira matarsa da wata boyayyiyar lamba aka shaida mata cewa mijin nata ya rasu.

Bayan zuwan jami’an tsaro, an gudanar da bincike a kan gawarsa inda aka gano cewar ya sha wahala kafin muturwa tasa, saboda irin raunuka da aka ji masa.

Iyalan mamacin sun yi mamakin yadda abokin da ya raka shi yin wanka bai dawo domin sanar da su rasuwar tasa ba.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Odiko Macdon, ya ce ba shi da masaniya a kan lamarin, saboda ba su samu wani rahoto daga ofishin ’yan sanda da ke Abak ba.