An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Shekwo wanda masu garkuwa suka sace da daren ranar Asabar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Dele Longe ne dai tun da farko ya tabbatar da sace shi daga gidansa dake Lafiya babban birnin jihar.
Wata majiya dake da kusanci da iyalan mamacin da ba ta amince a ambaci sunanta ba ce ta tabbatar da tsintar gawar tasa ranar Lahadi.
Sai dai ya zuwa yanzu jam’iyyarsa ta APC ba ta ce uffan ba game da sacewa da kuma kisan tsohon shugaban.
Kwamishinan ‘Yan Sandan ya ce, “Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa gidan shugaban APC kawanya da misalin karfe 11:00 na daren ranar Asabar kafin daga bisani jami’anmu su sami nasarar korarsu.
“Lamarin ya fi karfin garkuwa da mutane, saboda sun tafi da shi kuma ba su bukaci ko sisi ba a matsayin kudin fansa. Mun yi bincike daga baya kuma muka tsinci gawarsa dab da gidansa.
“Wannan abin takaici ne matuka, kuma ba za mu lamunta ba,” inji Kwamishinan ‘Yan Sandan.
Tuni dai rahotanni suka tabbatar da kai gawarsa dakin adana gawawwaki na asibiti, yayin da iyalansa kuma ke ci gaba da jimamin kisan gillar.
Mazauna yankin Bukan Sidi dake cikin birnin na Lafiya sun ce ‘yan bindigar sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi yayin harin domin kaucewa mayar da martani daga jami’an tsaro da kuma makwabta.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule da Sanata Umar Tanko Al-Makura sun mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.