✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar mutum 10 bayan harin ’yan bindiga a Kudancin Kaduna

An kai harin ne a Karamar Hukumar Zangon Kataf

Akalla gawarwaki 10 aka tsinta bayan wani harin ’yan bindiga a kauyen Unguwar Wakili da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Tuni dai majalisar Karamar Hukumar ta sanar da sanya dokar hana fita a yankunan Ungwan Juju da Mabuhu da Ungwan Wakili da kuma Zangon Uba.

Karamar Hukumar dai ta sanar da sanya dokar ce a cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Karamar Hukumar, Yabo Chris Ephraim, ya fitar.

Ya ce an sanya ta ne domin dakarun sojoji su sami zarafin dawo da zaman lafiya a yankin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ba ta magantu a kan lamarin ba.

Muna tafe da karin bayani…