✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar malamin cocin da ’yan bindiga suka sace a Kaduna

Gawar tashi da aka tsinta har ta fara rubewa

An tsinci gawar daya daga cikin malaman coci guda biyun da ’yan bindiga suka sace a jihar Kaduna a ranar Juma’ar da ta gabata.

Aminiya ta rawaito yadda aka sace Rabaran Fada John Mark Chietnum da Rabaran Fada Donatus Cleopas.

An sace su ne daga cocin King Catholic da ke Yadin Garu a Karamar Hukumar Lere da ke jihar, inda suka je wani aiki.

A cikin wata sanarwa da shugaban Kiristoci mabiya darika Katolika da ke Kafachan, Rabaran Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya fitar, ya ce duk da an kashe Chietnum, shi kuma Cleopas ya sami gudowa daga hannun wadanda suka yi garkuwar da su.

Ya ce an tsinci gawar Rabaran din ce, wacce har ta fara rubewa a ranar Talata.

Bayanai sun nuna an kashe shi ne tun a ranar da aka sace shi.

Kafin kisan nashi, Rabaran Chietnum shi ne Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Karamar Hukumar Jema’a, kuma mai rikon mukamin shugabancin na CAN a Kudancin Kaduna.

Sanarwar ta kuma ce za a yi bikin binne shi da misalin karfe 10:00 na safiyar Alhamis, a majami’ar St. Peter da ke Kafanchan.