Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da tsintar wani mutum mai shekara 50 a bakin kudiddifin unguwar Sallari a yashe, wanda daga bisani ya ce ga garinku nan.
Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya ba da sanarwa jim kadan bayan gano mutumin bakin ruwan.
- Afghanistan na bukatar kayan agajin Dala biliyan 5 a 2022 —MDD
- ‘Abin da ya sa na amince a yi min dashen zuciyar alade’
Hukumar ta kuma mika gawar mamacin ga wani dan sanda mai suna Kofur Jamilu Musa da ke ofishin ’yan sanda na Filin Hockey.
Kakakin hukumar ya kara da cewa hukumar ta yi nasarar ceto wata mata da danta daga wata gobara da ta tashi.
Matar mai suna Zainab Yusha’u da danta Sulaiman Usaini, sun makale a cikin gidansu bayan wutar ta tashi amma an yi nasarar ceto su hajaran-majaran.
Ya ce, “Mun samu kiran neman agaji daga wani mai suna Usman Nura, cewa gobara ta tashi a kan Titin Gwarzo zuwa Gidan Kaji.
“Nan take muka tura jami’anmu, bayan isarsu ne suka gano matar da danta sun makale a gidan da gobarar take ci.
“Bayan ceto su an mika su ga mijin matar mai suna Malam Usaini da ke unguwar Gidan Kaji,” inji shi.
Ya kara da cewa, bayan kokarin da jami’an hukumar suka yi, sun samu nasarar kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa gidajen da ke makwabtaka da wurin da gobarar ta tashi.