✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar jariri sabon haihuwa a bola

Jami’an ’yan sanda sun dauke wani jariri sabon haihuwa da aka jefar da shi a cikin wata bola a garin Fatakwal, Jihar Ribas. An tsinci…

Jami’an ’yan sanda sun dauke wani jariri sabon haihuwa da aka jefar da shi a cikin wata bola a garin Fatakwal, Jihar Ribas.

An tsinci gawar jaririn mai kwana daya da haihuwa ne a yashe a wani kwandon shara a kan titin Ikwerre a unguwar Mile 2 Diobu.

Mazauna yankin da suka ga gawar jaririn sun ce sun yi koro da ita ce a lokacin da suka je su zubar da shara a jujin.

Walikinmu ya ce kururuwar da rukunin farkon mutanen da suka ga jaririn suka yi ne ya ja hanaklin sauran mutane suka taru.

Majiyar ta ce an kuma tsinci wani sirinji da aka yi amfani da shi a kusa da gawar jaririn da aka jefar.

Sakataren Kwamitin Daraktocin Cibiyar Kare Hakki da Tabbatar da Gaskiya, Prince Wiro, wanda ya halarci wurin, ya yi takaicin jefar da jaririn, wanda ya ce tsabar keta da rashin imani ne.

Ana iya tunawa a makonnin baya wasu kanikawa tsinci gawar wani jariri da ya fara rubewa a wani filin zubar da shara a garin na Fatakwal.