An tsinci gawar wani dan Najeriya a jikin tayar wani jirgin sama mallakin kamfanin KLM da ya tashi daga Legas zuwa kasar Netherlands.
A cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Talata, an tsinci gawar ce a jikin tayar jirgin kirar Boeng 777 mai lamba PH-BQM a ranar Litinin.
- INEC ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Adamawa
- Rarara ya nemi kotu ta yi watsi zargin taurin bashin N10m da ake masa
Lamarin dai ya jawo muhawara sosai a kan yadda abin ya faru da kuma lokacin da ya faru.
Sanarwar ta KLM ta ce, “Yau da safe, mun tsinci gawar wani mutum a jikin tayar jirginmu kirar Boeng 777 mai lamba PH-BQM.
“Jirgin ya taso ne daga birnin Legas na Najeriya. Yanzu haka babu wanda ya san yadda mutumin ya samu darewa jikin tayar da kuma lokacin da ya hau, amma mun kaddamar da bincike a kan hakan.
“Ana zargin tsananin sanyi ne ya kashe mutumin,” in ji sanarwar.
Labarin dai ya jawo tarin tambayoyi kan yadda har mutumin ya samu damar shiga har wajen tashin jiragen sama na kasa da kasa ba tare da an gano shi ba
Daga cikin tambayoyin da ake yi dai akwai na ingancin tsaro a filayen jiragen saman na Najeriya da kuma ko mamacin ya hada baki ne da wasu ma’aikatan wajen har ya samu damar makalewa a tayar jirgin.