Iyalan wani dan kasuwa a Kano da ’yan bindiga suka sace, Yahaya Hassan Musa, sun kadu bayan an tsinci gawarsa a daji sa’o’i kadan bayan an biya kudin fansarsa Naira miliyan shida.
’Yan bindiga sun sace Yahaya ne a yankin Mopa na Jihar Kogi, ranar Alhamis din da ta gabata, yana dawowa daga harkokin kasuwancinsa a Kwatano a Jamhuriyar Benin, suka bukaci a biya su Naira miliyan 10, wanda daga bisani suka rage zuwa miliyan shida.
- An sanya na’ura mai ba da fatawa da Hausa a Masallacin Harami
- Sojoji sun kashe mayakan ISWAP sama da 100 a Tafkin Chadi
Wani dan uwansa mai suna Abubakar, ya ce, “’Yan bindigar sun bukaci in dauki kudin zuwa dajin Kabba.
“Da na kai kudin sai suka yi min kwatancen inda zan same shi, amma da na je wurin ban same shi, har na kwana a cikin dajin ni kadai.
“Washegari da safe sai wata mata da aka sace su tare da dan uwana ta kira ni a waya ta shaida min cewa ’yan bindigar sun kashe shi tun kafin a kawo kudin fansar, amma ba ta san a inda suka jefar da gawarasa ba.
“Na koma wani gari da ke kusa da dajin, inda na dauki hayar mafarauta muka shiga dajin neman gawarsa; bayan shafe tafiyar kilomitoci sai muka tsinci gawarsa a daji.”
Hassan ya bayyana cewa marigayin yakan bi jirgin sama a duk lokacin da zai yi tafiya, amma a wannan karon saboda karar kwana ya bi mota.
Ya bayyana cewa sun binne dan uwan nasa bayan tattaunawa da ’yan uwa a can saboda halin da suka tsinci gawar a ciki ya yi muni da yawa.