✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar dalibi a Kano bayan kwana 5 da batansa

An dai tsinci gawar tasa ne a wajen wani wurin hakan yashi a unguwar Mariri.

An tsinci gawar wani dalibin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta garin Wudil (KUST) a jihar Kano, Ahmad Abubakar Idris, kwanaki biyar bayan an ba da rahoton bacewarsa daga makarantar.

Mai kimanin shekaru 22 a duniya, dalibin wanda ke matakin aji uku a Sashen Koyar da Ilimin Sinadarai ya bace ne tun ranar Asabar din da ta gabata, lokacin da ya tafi kasuwar wayoyin hannu ta Farm Centre dake Kano da nufin sayen waya.

An dai tsinci gawar tasa ne a wajen wani wurin hakan yashi a unguwar Mariri dake kusa da birnin Kano, kuma binciken ’yan sanda ya alakanta mutuwarsa da wani abokin karatunsa wanda suke tare da shi kafin mutuwar.

Da yake zantawa da Aminiya, mahaifin yaron, Abubakar Idris ya ce suna zargin an kashe masa dan nasa ne saboda kudin da suke hannunsa a lokacin.

Abubakar ya kuma ce ranar Asabar aka kira shi aka sanar da shi labarin batan dan nasa, lamarin da ya sa ranar Alhamis ya tafi Kano takanas tun daga Abuja inda yake zaune da nufin sanar da ’yan sanda.

Ya kara da cewa lamarin ya fara ne tun lokacin da aka turo masa da kudi don ya saya wa dan uwansa waya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka cafke mutum biyu wadanda ake zargin da hannu a ciki.

Ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Sama’ila Dikko ya ba da umarnin a mika batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka domin fadada bincike.