✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar daliba a Jami’ar Bayero

Dalibar ta rasu a dakin kwanan dalibai mata mai suna Ramat da ke Jami'ar.

An samu gawar wata dalibar ajin karshe kwance a dakunan kwanan dalibai na Jami’ar Bayero da ke Kano.

Hukumomin Jami’ar Bayero sun ce marigayiyar Mercy Sunday, da ke aji na hudu a Sashen Kimiyyar Siyasa, ta rasu ne ranar Litinin da dare a dakin kwanan dalibai mata mai suna Ramat da ke a jami’ar.

Shugaban Sashen Kula da Jin Dadin Dalibai na jami’ar, Dokta Shamsudeen Umar, ya ce dalibar ta yi jinyar zazzabi a asibitin makarantar, daga bisani ya sake dawo mata ranar Litinin da dare inda ya yi ajalinta.

A cewarsa, “Ta yi fama da rashin lafiya inda aka kwantar da ita a asibitin jami’ar; bayan ta samu sauki aka sallame ta, ta koma dakin kwanan dalibai.

“Amma ciwon ya dawo mata ranar Litinin da dare; kafin wayewar gari ranar Talata ta mutu,” inji shi.

%d bloggers like this: