✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige Trump a karo na biyu

Trump ya kafa tarihin zama Shugaban Amurka na farko da aka tsigewa sau biyu

Shugaba Donald Trump ya kafa tarihi a matsayin Shugaban kasar Amurka na farko da aka tsige sau biyu.

Mafi yawan ’yan Majalisun sun kada kuri’a a ranar Laraba, don tsige Donald Trump, wanda saura mako daya ya kammala wa’adin mulkinsa.

Mutum 217 daga cikin mambobin Majalisar 433, sun kada kuri’a kan a tsige Trump.

Akalla ’yan jam’iyyarsa ta Republican 10 ne suka sauya sheka zuwa Democrat.

Ana sa ran Trump, mai shekaru 74 a duniya, zai fuskanci zai gurfanarwa a gaban Majalisar don a yi masa hukunci ne bayan ya sauka daga mulki.