Mambobin Majalisar Dokokin Jiihar Gombe sun tsige shugabansu, Abubakar Sadiq Kurba daga mukaminsa.
An tsige shi ne a ranar Talata bayan 16 daga cikin 24 na mambobin majalisar sun kada kuri’ar amincewa da hakan.
- An tsige Shugaban Majalisar Imo
- An tsige Shugaban Majalisar Edo
- Yaki da COVID-19 ya lakume biliyan daya a Gombe
Mataimakin Shugaban Majalisar, kuma mamba mai wakiltar mazabar Kwami ta Yamma, Siddi Buba ne dai ya jagoranci zaman da ya kai ga tsige Shugaban Majalisar.
Zauren bai yi wata-wata ba ya maye gurbinsa da Mamba mai wakiltar mazabar Akko, Abubakar Muhammad Luggerewol a matsayin sabon Shugaban Majalisar.
Abubakar ya dare kujerar ne bayan 15 daga cikin ’yan majalisar sun amince da shi a matsayin da murya daya.
Tuni dai Mataimakin Shugaban Majalisar, Siddi Buba ya rantsar da shi kuma ya fara aiki.
Bugu da kari, sauyin ya yi tafiyar ruwa da kujerar Jagoran Majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Pero-Chonge, Samuel Marcus, wanda shi kuma aka maye gurbinsa da Yarima Ladan Gaule, mai wakiltar mazabar Kaltungo ta Gabas.