Majalisar Dokokin Albaniya, ta tsige Shugaban Kasar, Ilir Meta, shekara guda gabanin kawo karshen wa’adin mulkinsa.
Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar da tabbatar da dalilai na cewa Shugaba Meti ya taka dokokin kasar, lamarin da ya sanya ta kira wani zama na musamman ta tsige shi a ranar Laraba.
Da yake gabatar da jawabi gabanin fara kada kuri’ar tsige shugaban a zauren Majalisa, Firaiministan Kasar, Edi Rama ya ce Shugaba Meta ya saba wa kundin tsarin mulki ta hanyar taka dokokin zaben kasar yayin zabukan ’yan Majalisar da aka gudanar a watan Afrilun da ya gabata.
“Ilir Meta ya ci amanar kujerar Shugaban Kasa, sannan ya wulakanta kundin tsarin mulkin kasa,” a cewar Edi Rama.
Mambobin Majalisar 104 ne suka jefa kuri’ar tsige Shugaba Meta yayin da bakwai suka jefa ta su kuri’ar sabanin haka.
Sai dai a yanzu za a saurari hukuncin ta Kotun kundin tsarin mulkin kasar za ta zartar nan da watanni uku kasancewar ita kadai ke da hurumin tabbatar da tsigewar da aka yi wa shugaba Meta.
Wata sanawar da Shugaba Meta ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Tedi Blushi, ta bayyana tsigewar a matsayin wasan yara da ta ci karo da doka.
Kafar watsa labarai ta Aljazeeta a ruwaito cewa, a yayin da ake Majalisar ke gudanar zama na musamman da ta kira kan tsigewar, Shugaba Meta ya ci gaba da gudanar da harkokinsa na yau da kullum, inda ya bayar da lambar yabo a wani taron kade-kade da wake-wake da aka gudanar a kasar.