Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Rauf Olaniyan daga mukaminsa a safiyar Litinin.
Majajlisar ta tsiga mataimakin gwamnan ne bisa shawarar kwamitin mutum bakwai da Babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Munta Abimbola, ya kafa domin bincikar shi kan aikata ba daidai ba.
Daukacin mambobi 23 da ke majalisar sun amince da tsigawar wadda ta fara aiki ne nan take.
Rahoton da kwamitin ya gabatar wa majalisar a ranar Litinin ya ce, an same da aikata duk laifuka uku da ake zargin shi.