✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsige Hakimin Kankara saboda hada baki da ’yan bindiga

Jama’a na jira su ga matakin da za a dauka a kansa tun da an kama shi da laifin.

Majalisar Masarautar Katsina ta tsige Sarkin Pauwan Katsina kuma Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal bisa kama shi da laifin hada baki ’yan bindiga.

Ana ganin yankin Kankara wanda hakimincinsa ke hannun Sarkin Pauwan Katsina a matsayin cibiyar ayyukan barayin shanu da masu garkuwa da mutane tare da kisan ba gaira babu dalili.

Al’ummar Masarautar sun dade suna gunaguni da zargin hakimin da alaka tare da goyon bayan barayin shanun.

Wani mazaunin garin Kankara ya shaida wa Aminiya cewar ko a kwanakin baya lokacin da aka kawo wa yankin hari har aka kashe wasu mutane, jama’a sun kama wasu daga cikin ’yan bindigar suka mika wa hakimin.

“Amma abin mamaki, maimakon ya kai su ga hukumar da ta dace, kawai sai dai muka rasa yadda aka yi, muka sake ganin Fulanin nan suna yawo. Kai abubuwa dai ga su nan babu dadin ji,” a cewarsa.

Wadannan zarge-zarge da jama’a ke yi suka sa Masarautar Katsina ta fara dakatar da hakimin, ta kafa kwamiti don binciko gaskiyar lamarin.

Bayan kwamitin ya kawo rahatonsa kuma aka tabbatar da laifin da ake zargin da sa aikatawa, nan take Masarautar ta tsige shi daga sarautarsa.

A halin yanzu jama’a sun zura ido su ga matakin da za a dauka a kansasa nan gaba bayan samun shi da laifin taimaka wa ’yan bindiga.