✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara.

Kasar Qatar babbar mai shiga tsakani a rikicin Isra’ila da kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa an tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza da kwana guda har zuwa ranar Juma’a.

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Majed al-Ansari ne ya sanar da wannan labari a cikin wata sanarwa da ya fidda, inda ya ce an cimma wannan matsaya ne tare da tsoma bakin kasashen Amurka da kuma Masar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin cikar wa’adin yarjejeniyar kwanaki shida da bangarorin da ke gwabza fada suka cimma wanda ya kawo karshe da Asubahin ranar Alhamis.

Tuni ma dai kungiyar Hamas ta tabbatar da wannan labari na tsawaita wa’adin yarjejeniyar wacce ke ba da damar isar da kayan agaji a zirin Gaza.

A daya gefe kuma sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra’ila inda yake ganawa da firaminista Benjamin Netanyahu kan rikicin da ya barke tun a ranar bakwai ga watan Oktoban da ya gabata.

Isra’ila ta sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan

Rundunar sojin Isra’ila ta tsare aƙalla Falasɗinawa 40 a wani samame da ta kai Yammacin Kogin Jordan da safiyar ranar Alhamis, a cewar Ƙungiyar Fursunoni ta Falasɗinawa.

Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.

Tashin hankali na ƙaruwa a Yammacin Kogin Jordan a yayin da sojojin Isra’ila ke kai hare-hare Zirin Gaza tun bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Hare-haren da Isra’ila ta kwashe kwana 55 tana kai wa Gaza sun yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara.

Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra’ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.