Shugaban Masar, AbdelFattah al-Sisi ya sake tsawaita dokar ta-bacin da ya sanya a fadin kasar da watanni uku daga ranar Litinin.
Jaridar Ahram ta kasar ta ambato shugaban yana cewa, “Sojoji da ‘yan sanda za su dauki matakan da suka zama wajibi wajen yaki da ta’addanci da samar da tsaro a duk fadin kasa, tare da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.”
A bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar dai, dole sai shugaban ya sami sahalewar Majalisar Dokokin kasar kafin tsawaita dokar ya fara aiki.
Shugaba AbelFattah ya fara kakaba dokar ta-bacin ne ta farko tun a watan Afrilun 2017 bayan wasu hare-haren bama-bamai a kan wasu majami’u a lardunan Gharbiya da Alexandria dake arewacin kasar.
Rahotanni sun ce akalla mutum 47 suka hallaka yayin da sama da 120 kuma suka jikkata yayin harin a wancan lokacin.
Kasar Masar dai ta yi ta fuskantar hare-haren ta’addanci da suka yi sanadiyyar rasa ran daruruwan jami’an tsaro tun bayan da aka hambarar da gwamnatin shugaba Mohammed Morsi a 2013.
Kungiyar mayakan yankin Sinai mai suna Wilayat Sinai ce dai ke daukar alhakin akasarin hare-haren da ake kaiwa.
A wani labarin kuma, kasar ta kaddamar wani gagarumin shiri na fatattakar ta’addanci a kasar tun a watan Fabrairun 2018 inda ta kashe akalla ‘yan ta da kayar baya 1,000.