✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsaurara tsaro a Binuwai gabanin rantsar da sabon gwamna

Za a rantsar da sabon gwamnan a ranar 29 ga watan Mayu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai ta bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro gabanin bikin rantsar da sabon gwamna a ranar 29 ga watan Mayu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Okoro Alawari Julius, ya umarci dukkan manyan jami’an yankuna da su tabbatar da ingantaccen tsaro a daukacin jihar.

Julius a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar, SP Catherine Anene, ta ce umarnin yana cikin tsarin ayyukan da aka tsara.

Kwamishinan ’yan sandan ya jaddada cewa ya kamata a bai wa wajen taron bikin rantsuwar isassun jami’ai da kayan aiki domin tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro.

“An gargadi dukkan ’yan sanda da su kasance masu kwarewa sosai wajen gudanar da ayyukansu.

“Rundunar tana kuma sanar da jama’a cewa za a datse hanyar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) a wani bangare na kokarin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa.

“Don haka an yi kira ga jama’a da su kasance masu bin doka da oda tare da bai wa jami’an hadin kai.

“An gargadi mutane da su guji yin abin da bai dace ba a lokacin bikin rantsuwar,” in ji kwamishinan.