✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsaurara tsaro kafin zuwan Buhari Adamawa

An tsaurara tsaro a jihar don tabbatar da komai ya tafi lafiya yayin ziyarar shugaba Buhari.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta tsaurara matakan tsaro gabanin ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai jihar.

Rundunar ta bukaci jami’anta da su nuna kwarewa tare da tabbatar da kare hakkin dan Adam a yayin ziyarar ta shugaban kasa.

Wannan na dauke ne cikin sanarwar da kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Asabar a Yola.

Ya ce rundunar ta samar da karin jami’an tsaron hadin guiwa ne don tabbatar da komai ya gudana a yayin ziyarar ta Buhari.

“Ana sa ran za su sanya ido tare da nuna kwarewa a lokacin da shugaban kasa zai kawo ziyara.

“Hukumar ’yan sandan Nijeriya za ta hada kai da masu ruwa da tsakin jihar don tabbatar da komai tafi daidai a ziyarar Buhari.”

Nguroje, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya shawarci masu amfani da hanyar da ta taso daga Sangere-Numan zuwa titin Yola da su kaurace wa hanyar a ranar da Buhari zai zo.

Su kuma wadanda suka taso daga titin Yola zuwa titin filin jirgin sama, su bi hanyar rukunin gidajen kwamishinoni don kauce wa cunkoson ababen hawa.