✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare ɗan jarida a gidan yari kan sukar Gwamnatin Kano

Ana zargin ɗan jaridar da ɓata sunan hadimin gwamnan.

Wata Kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, ta bayar da umarnin aike wani ɗan jarida gidan yari, kan wallafa wasu faifan bidiyo na sukar wani hadimin Gwamnan Kano.

Tun da farko ’yan sanda sun kama ɗan jaridar mai suna, Mukhtar Dahiru wanda ma’aikacin gidan rediyon Pyramid FM ne da ke Kano.

Ana tuhumarsa ne kan ƙarar da mashawarcin Gwamnan Kano, kan harkokin siyasa, Anas Abba Dala ya yi.

Hadimin, ya yi zargin cewa Mukhtar ya wallafa a shafinsa cewa shi jahili ne, tare da ɓata masa suna ta hanyar masa ƙage cewar ya yi wa wara yarinya cikin shege.

Har wa yau, an zargi ɗan jaridar da ɗora wasu bidiyon a shafinsa na Facebook kam5 zargin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da cin hanci da rashawa.

Ɗan jaridar ya wallafa wani sautin murya da wani ɗan adawa, ya zargi Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, cewa yana yaudarar mutane da sunan tausaya musu bayan ya kasance almubazzari.

Kazalika, an ruwaito cewar ya wallafa cewar hadimin gwamnan Kano, ya yi zargin cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ba asalin ɗan Najeriya ba ne.

Sai dai dan jaridar, ya musanta laifukan da ake zarginsa na haɗa baki da ɓata suna da kuma zagi.

Laifukan dai sun saɓa da sashe na 97 da 391 da 115 na Kundin Pinal Kod.

Alkaline Kotun Mai Shari’a Umma Kurawa, ta bayar da umarbin tsare ɗan jaridar a gidan gyaran hali.

Ta ɗage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Satumba, 2024 don yanke hukunci kan yiwuwar bayar da belin ɗan jaridar.