✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsare tsohon soja saboda ‘yi wa ‘yar shekara 4 fyade’

Wani tsohon soja mai mukamin Kyaftin na hannun ‘yan sanda bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara hudu fyade. Hukumar kare hakkin Dan Adam ta…

Wani tsohon soja mai mukamin Kyaftin na hannun ‘yan sanda bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara hudu fyade.

Hukumar kare hakkin Dan Adam ta Basic Right Initiative ta hannanta shi ga Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kuros Riba saboda lamarin da ya faru a unguwar BigQuo da ke Karamar Hukumar Kalaba.

Makwabcin wanda ake zargin ya shaida wa Aminiya cewa yarinyar kan kira wanda ake zargin da suna kawu amma ya yaudare ta zuwa cikin gida.

Ya ci gaba da cewa wanda ake zargin “ya tura matarsa taje kasuwa ta yi musu cefane amma ta dawo ta iske aika-aikan.”

Zargin ya fito fili ne bayan kanen yarinyar ya shaida wa mahaifiyarsu cewa ya ga ‘kawu’ yana sa mata hannu a mutuncinta.”

Jin hakan ne ya sa makwabta sanar da Basic Right wadda ta kama kuma ta mika wanda ake tuhuman a hannun ‘yan sanda.

Shugaban kungiyar, Barista James Ibor ya tabbatar wa Aminiya cewa ‘yan sanda na bincikar mutumin, ita kuma yarinyar an kai ta asibiti domin a duba lafiyarta.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo ta ce “E yana hannunmu ana bincikar sa, da zarar an gama za a mika shi kotu,” inji ta.