Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari bisa zargin sa da yi wa agolarsa mai shekara 14 fyade.
Babbar Kotun Majistaren ta ba da umarnin a tsare mahaucin mai shekara 40 ne bayan an gurfanar da shi a gabanta kan lalata karamar yarinyar.
- An bayar da belin wanda ake zargi da satar wayar N36,000 a kan N500,000
- Ko sisi ba za mu biya diyya kan daliban Kagara ba – Gwamnatin Neja
- Gobara a sansanin ’yan gudun hijirar Borno ta hallaka jariri, ta kona gidaje 620
Babban alkalin kotun, P.E. Nwaka ya ba da umarnin a tsare magidancina a gidan yarin da ke Ikoyi a jihar Legas, sannan ya dage sauraron karar har sai ranar 18 ga watan Fabrairu.
Tun da farko, lauya mai shigar da kara, ASP Thomas Nurudeen ya fada wa kotun cewa mutumin ya aikata laifin ne a watan Janairu a unguwar Ilasamaja da ke Legas.
Nurudeen ta ce yarinyar ta fada wa mai ba ta shawara a makaranta ne cewa mahaifin na ta ya lalata ta.
Ya ce mai ba ta shawara ta kai karar lamarin ga ma’aikatar matasa da ci gaban zamantakewar jihar Legas wacce ta kai ta ga ‘yan sanda.
Mai Shari’a Nwaka ya yi watsi da hanzarin magidancin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Laifin, in ji shi, ya ci karo da sashi na 137 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas, ta shekarar 2015.